in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar MERS ba ta da karfi sosai wajen yaduwa tsakanin Bil'adam, in ji kungiyar WHO
2015-06-06 13:51:27 cri
Kakakin kungiyar kiwo lafiya ta duniya (WHO) Christian Lindmeier ya bayyana a jiya Jumma'a 5 ga wata cewa, bisa cutar SARS, yanzu ana iya ganin cewa, cutar MERS ba ta da karfi sosai wajen yaduwa tsakanin bil'adam, a sabili da haka, bai kamata mutane su damu sosai kan wannan cuta ba.

Mista Lindmeier ya bayyana cewa, kawo yanzu Sin da Koriya ta Kudu sun riga sun dauki kwararan matakai wajen tabbatar da kebewa da kuma ba da jiyya ga wadanda ake zaton cewa sun kamu da cutar MERS, kuma ana sa ido sosai kan wadanda suka taba yin mu'amala da wadannan mutane, domin kebe su zuwa wurare na daban cikin yanayi mai dacewa.

Duk da haka kuwa, mista Lindmeier ya kara da cewa, kwayoyin cutar MERS, wasu sabbin kwayoyi ne. Tun da aka gano su a shekarar 2012, ana ta yin nazari a kai, amma watakila kwayoyin za su rika sauyawa a nan gaba.

A jiya, cibiyar shawo kan cututtuka ta Sin ta sanar da cewa, an riga an kammala aikin yin nazari kan layin DNA na kwayoyin cutar MERS.

Dadin dadawa, a jiya kuma, ma'aikatar kiwon lafiya ta Koriya ta Kudu ta bayyana cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar MERS ya karu zuwa 41, a cikinsu kuma, guda hudu sun mutu, ban da haka, yawan mutanen da aka kebe su zuwa wuri na daban ya kai 1820 a kasar.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China