in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta kawar da cutar shan inna a shekarar 2017
2015-01-22 10:42:09 cri

Kasar Najeriya za ta kawar da cutar shan inna a shekarar 2017, idan har ba a sake ganin bullowar cutar ba nan da watanni shida masu zuwa, in ji wani jami'i a ranar Laraba.

Ya zuwa yanzu, watanni shida ke nan da ba'a yi rajistan wani nau'in cutar ba a kasar. Nau'in cutar guda na baya bayan nan, an gano shi ne a cikin watan Yulin shekarar 2014.

Mista Mohammed Ado, darektan cibiyar ci gaban kiwon lafiya jama'a ta kasa, ya nuna cewa, Najeria, kasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika, ta samu ci gaba sosai wajen kawar da cutar shan inna, kana za ta yi bincike kan wasu sauran fannoni wadanda daga cikinsu, ci gaban da aka samu zai taimaka wajen kyautata da karfafa aikin mu. Babu yaro ko guda da ya samu nakasa sakamakon cutar shan inna tun yau da watanni shida a Najeriya. Baya ga haka, tuni mun fara kidayar ranaku har zuwa ranar 24 ga watan Yulin shekarar 2015, ranar da za'a kawar da cutar shan inna a Najeriya, in ji mista Ado. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China