Har wa yau, tashar yanar gizo ta internet mai watsa labarai mai suna Tauraro ta Rasha ta ba da labarin cewa, a jiya laraba sakataren shugaban kasar Rasha mai kula da batun watsa labarai, Dmitri Peskov ya bayyana cewa, fadar Kremlin ta damu sosai kan rikicin da dakarun Ukraine suka yi a gabashin kasar kuma za ta dauki mataki bisa matsayinta kan yanayin da ake ciki.
A kwanan baya, yanayin tsaro a gabashin Ukraine ya tabarbare inda sojojin kasar suka kara yin musayar wuta tsaknin su da dakarun wurin.(fatima)