Cikin kulaflikan da suka fara nuna sha'awar hada gwiwar cinikayya da kamfanonin kasar Sin, hadda zakaran kasar Jamus Bayern Munich, wanda a 'yan kwanakin nan ya bayyana shirin sa na fara zantawa da kamfanin cinikayya ta yanar Gizo na nan kasar Sin wato Alibaba.
Rahotanni sun bayyana cewa kulaf din na fatan kulla wata alaka da za ta bashi damar fara sayar da rigunan 'yan kwallo, masu dauke da sunayen 'yan wasa da aka rubuta sunayen su da sinanci. Kaza lika kulaf din na da burin buga wasannin sada zumunta da Inter Milan, da Valencia da kuma zakaran kulaflikan kasar ta Sin wato Guangzhou Evergrande, cikin watan Yuli mai zuwa a matsayin wata hanya ta fadada karbuwar sa a kasar ta Sin.
Da yake karin haske game da wannan batu, shugaban kulaf din na Munich Karl-Heinz, ya ce Sin ta zama babbar kasuwa ga wasan kwallon kafa.
Wasu alkaluman bincike sun nuna cewa ya zuwa watan Satmbar bara, kulaflikan turai 32 sun bude shafukan su a dandalin sada zumunta na Weibo na kasar Sin, wanda ke kwatankwacin shafin Twitter, kuma cikin wadannan kulaflika 32, 10 daga cikin su na buga gasar Serie A ne ta kasar Italiya, sai 7 dake buga Bundesliga, da La Liga da kuma gasar Premier ta kasar Ingila.
Kididdiga ta nuna cewa cikin dukkanin wadannan kulaflika, Bayern ce ke kan gaba a yawan mabiya, yayin da Schalke ke biye da mabiya 950,000, sai Borussia Dortmund mai mabiya 715,000.(Saminu Alhassan)