150528-xavi-zai-bar-kungiyar-barca-bello.m4a
|
Kafin haka dan wasan mai shekaru 35 a duniya, ya sanar da niyyarsa ta kawo karshen kwallo a Barcelona, bayan ya bugawa kungiyar wasanni 764, tare da taimakawa kungiyar lashe kambin gasar La Liga karo 8, da daga kofin kasar Spaniya karo 2, gami da lashe gasar cin kofin zakarun Turai har karo 3. Yanzu haka dai an tabbatar da cewa Hernandez zai ci gaba da taka leda a kasar Qatar kafin ya yi ritaya.
Kafin kammala wasan Barca da Deportivo da ya gudana a karshen gasar La Liga, an yi sauyin Hernandez, inda lokacin da yake fita daga wasan masoya da magoya bayan kungiyar ta Barca su kimanin 98,000 suka rika sowa, tare da jinjinawa Xavi.
Bayan da aka kammala wasan, Xavi da abokan taka ledar sa sun tsaya cikin filin wasan, domin kallon wani fim tare da sauran magoya baya, fim din da ke nuna nasarori da girmamawa ga Xavi. Daga bisani Xavi ya yi jawabin godiya domin nuna farin cikin sa ga goyon bayan da aka nuna masa.
Kafin hakan, Xavi ya riga ya bayyana fatansa na ci gaba da samun horo na zama mai horsa da 'yan wasa, ta yadda zai samu damar komawa kungiyar ta Barca nan gaba a matsayin kocin kungiyar. Amma kafin nan, yanzu zai ci gaba da taka leda a Barca, a wasan da za ta yi da Bilbao a ranar Asabar mai zuwa domin neman lashe King's cup, gami da wasan da zata buga da Juventus a birnin Berlin a makon da zai biyo baya, a kokarin neman lashe kofin zakarun Turai.
Bisa tarihi, an haifi Xavi Hernandez ne a birnin Barcelona a shekarar 1980. Baban Xavi, wanda kwararren dan wasan kwallon kafa ne, ya yi fatan ganin dan sa ya gaje shi a kwarewar taka leda, don haka ya kan halarci wasan da Barca ke bugawa tare da Xavi, tun yana da shekaru 4 da haihuwa. Abin da ya sanya Xavi matukar sha'awar kwallon kafa.
A shekarar 1989, kulob din Barcelona ta kafa cibiyar horar da 'yan wasa ajin matasa a La Masia. Baban Xavi da dansa wanda a lokacin ke da shekaru 9 sun ziyarci cibiyar, sai dai ba a karbi Xavi ba domin karancin shekarun sa. Amma shekaru 2 bayan haka, yayin da Xavi ya cika shekaru 11 da haihuwa, cibiyar horaswa ta La Masia ta karbe shi bisa kwarewar da ya nuna, duk kuwa da cewa ana karbar 'yan wasa ne da suka kai shekaru 13.
Bayan samun horo a wannan cibiya, a shekarar 1998, Xavi da ke da shekaru 18 a lokacin, ya fara buga kwallo a matsayin daya daga cikin kwararrun 'yan wasan kungiyar Barca. Kuma wanda ya sanya shi cikin kungiyar shi ne Louis van Gaal, shahararren mai horas da 'yan wasan kwallon kafa wanda ke jagorantar kungiyar Barca a lokacin.
Kasancewar Xavi ya fara taka leda a Barca tun yana da sauran yarinta, hakan ya sa shi da sauran abokan wasan sa da yawa zama manyan kusoshi a fagen wasan kwallon kafa a kulaf din. Ga misali, Guardiola, da Luis Enrique, wadanda suka kasance manyan masu horar da 'yan wasa a kungiyar ta Barca na da da na yanzu, dukkansu sun taba taka leda tare da Xavi.
Zuwa yanzu, Xavi ya kwashe shekaru 17 yana taka leda a kulob din Barcelona, sa'an nan idan an lasafta shekarun da ya kwashe yana taka leda a ajin matasan kungiyar, za a iya cewa ya shafe shekaru 24 yana takawa kungiyar kwallo. Don haka ya ganewa idanunsa yadda kungiyar ta samu nasarori da karfi cikin tsahon lokaci, haka kuma ya taba ganin yadda kungiyar ta ci karo da koma baya a wasu lokuta. Amma duk da haka, bai taba nuna burin bari kungiyar ba.
A shekarar 1999, tauraron Xavi ya haskaka sosai, a gasar kwallon kafa ta matasan duniya, lamarin da ya sanya AC Milan gayyatar sa, da alkawarta ba shi albashi na Euro miliyan 1.8, kudi mai tsoka kwarai idan an kwatanta da albashin da yake dauka a Barca, wato Euro dubu 180 kacal. Amma duk da haka Xavi ya ki zuwa AC Milan, domin matukar kaunar sa ga kungiyar Barca, da kuma irin burin sa na ganin ya taka rawar gani a kungiyar.
Har ila yau, a kakar wasanni ta 1999, an sanya Xavi mai shekaru 20 a lokacin, ya fara buga wasa a tsakiyar kungiyar, lamarin da ya sanya shi fara zama ginshiki a kungiyar.
Yanzu haka dai bayan shekaru 17 ya na taka leda a Barca, Xavi ya bayyana niyyarsa ta barin kungiyar. Matakin da ya zamo tamkar shelanta ritayarsa ne, domin ya riga ya tsufa, kuma zuwan sa Qatar, zai zama dama ta neman kudi gare shi, amma ba wai neman ci gaba a fannin taka leda ba. Duk da haka dai mai yiwuwa ne Xavi ya sake komawa kungiyar Barca a wata rana, kamar yadda ya bayyana niyyarsa ta zaman babban kocin kungiyar a nan gaba.(Bello Wang)