in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
PSG ta daga kofuna 3 a kakar wasa ta bana
2015-06-04 09:23:54 cri
Kulaf din Paris Saint-Germain na kasar Faransa, ya samu nasarar daukar kofuna 3 a kakar shekarar nan ta 2014 zuwa 2015, bayan da a ranar Asabar din da ta gabata, ya cika wannan nasara lokacin da ya doke Auxerre da ci 1 mai ban haushi a wasan karshe na gasar kalubalen kasar Faransa.

Wannan ne dai karo na 9 da PSGn ta dauki wannan kofi, inda take biyewa Marseille wadda ta dauki kofin sau 10.

Kafin hakan kulaf din PSG ya dauki kofin Ligue 1 a farkon watan jiya. Baya ga "Trophee des Champions" wanda ya dauka a watan Agustar da ya gabata. Hakan na nufin dai PSG ce ta wawashe dukkanin kofunan da aka fafata neman su a kakar ta bana a Faransa, ita ce kuma ta biyu cikin kulaflikan Turai da suka samu irin wannan nasara.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China