in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wolfsburg ta kafa tarihi a gasar German Cup
2015-06-04 09:25:14 cri
Kulaf din Wolfsburg na kasar Jamus ya dauki kofin German Cup na bana, bayan da ya samu nasarar doke Dortmund da 3 da 1, a wasan karshe da suka buga a ranar Asabar.

Wannan ne kuma karo na farko da Wolfsburg din ta dauki wannan kofi, a kuma gabar da wasu daga 'yan wasan kungiyar kamar su Zhang Xizhe ke jiran damar su a wannan kungiya ta Wolfsburg, wadda ke taka leda a gasar Bundesliga.

Wolfsburg dai ta samu nasara kan Dortmund ne cikin kwallayen da ta zura a raga cikin mintuna 16, wanda hakan ya ba ta damar kasancewa a matsayin farko, na ajin kwararrun kulaflikan kasar Jamus, kana hakan ya bata damar shiga gasar zakarun Turai ta gaba.

Game da makomar sabbin 'yan wasa irin su Zhang wanda ya fara taka leda a Wolfsburg cikin watan Disambar bara, dan wasan ya shaidawa majiyar mu cewa zai sanya ido ya ga yadda za ta kaya a kakar badi, yana mai cewa zai kara azama a lokacin hutun bazara, domin cimma karin nasarori a fannin sana'ar sa.

Zhang dan shekaru 24 da haihuwa ya kara da cewa, zaman teburi ba abu ne da ya yi tsammanin zai dau lokaci yana yi a Wolfsburg ba. Ya ce yana sa ran samun cikakkiyar damar shiga a dama da shi a fagen wasannin da kulaf din na sa zai taka nan gaba kadan.

Sai dai wasu manazarta suna ganin rashin samun damar buga wasa ga 'yan wasa irin su Zhang, ba abu ne da zai bada mamaki ba, duba da cewa Wolfsburg din na da tsari da 'yan wasa da tun farkon kakar bana ke samarwa kulaf din manyan nasarori, inda kulaf din ya fara da lashe wasanni 3, da kunnen doki daya tun farkon gasar Bundesliga.

Hakan ya sa irin wadannan masu fashin baki ke ganin Zhang wanda ya zamo zakaran 'yan wasan kwallon kasar Sin na shekarar 2012, zai dan dau lokaci, da juriya kafin ya kai ga samun cikakken gurbi a fagen gasar Bundesliga karkashin kulaf din na Wolfsburg.

Zhang dai na cikin manyan 'yan wasa 4 daga kasar Sin, wadanda suka samu zarafin shiga manyan kungiyoyin kwallo na kasar Jamus. Sauran 'yan wasa Sinawa dake buga Bundesliga sun hada da Yang Chen, da Shao Jiayi, da kuma Hao Junmin. Shi ne kuma na farko cikin shekaru 3 da ya samu gurbi a manyan kulaflikan dake Turai, tun bayan da Hao Junmin ya bar kulaf din Shalk 04 zuwa gida kasar Sin a shekarar 2011.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v PSG ta daga kofuna 3 a kakar wasa ta bana 2015-06-04 09:23:54
v Xavi zai bar kungiyar Barca 2015-05-27 10:38:09
v Bayern Munich zai tattauna da kamfanin Alibaba 2015-05-27 10:36:55
v Alves ya bayyana yiwuwar barin Barcelona 2015-05-27 10:31:33
v Real Madrid ta sallami Ancelotti 2015-05-27 10:30:39
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China