Alves mai shekaru 32 da haihuwa, ya fara bugawa Barcelona tamaula ne bayan barin sa Sevilla a shekarar 2008. A wannan gaba dan wasan wanda ga alama ke ganin laifin yadda Barcelona ta gaza martaba shi yadda ya kamata, ya ce ba shi da niyyar sake bugawa kulaf din kwallo da zarar ya kammala kwantiragin sa na wannan shekara.
Tun dai watanni 2 da suka gabata ne wata 'yar uwar sa ta bayyanawa taron manema labaru cewa Alves da Barcelona, sun gaza cimma matsaya game da sake tsawaita zaman sa a kulaf din. A kuma wannan gaba 'yan kwanaki da mikawa kulaf din kofin La Liga na bana, shi ma Alves ya sake nanata waccan magana.
A cewar sa ba shi da wata manufa ta kawo Baraka ga kungiyar, amma ya zama dole gare shi ya kare kimar sa a matsayin sa na dan kwallo. Ya ce duk da cewa yana da burin ci gaba da murza leda a Barcelona, a hannu guda kulaf din na sa bai nuna wata sha'awa ta sake sabunta kwantiragin na sa ba, har sai da FIFA ya kakabawa kulaf din takunkumin hana sayen 'yan wasa, don haka a ganin sa dole ce ta sanya Barcelonan neman sabunta kwangilar ta sa a wannan lokaci.
Ya ce zaman sa a Barca na da alaka ne da martabar da kulaf din wanda ya bugawa kwallo shekaru kusan 7 ke nuna masa, amma idan har hakan ba ta samu ba, to fa babu abinda ya kamace shi, illa ya koma wani wurin na daban inda za a martaba basirar sa.(Saminu Alhassan)