in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kira taron Afirka na dandalin tattalin arzikin duniya a Afirka ta Kudu
2015-06-01 14:50:25 cri

Daga ranar Laraba zuwa Jumma'a mai zuwa ne za a gudanar da taron nahiyar Afirka, karkashin inuwar dandalin tattalin arzikin duniya karo na 25 a birnin Capetown na kasar Afirka ta Kudu, taron da ke da taken "Matakan baya da na yanzu, na yadda za a daidaita makomar nahiyar Afirka".

Taron da za a kira a birnin Capetown na kasar Afirka ta Kudu, zai samu halartar wasu manyan kusoshi 1250 daga kasashe 75, wadanda kuma ke da kwarewa a fannin cinikayya, da siyasa, da harkokin ilimi, da ayyukan raya al'umma, da na watsa labaru. Idan an yi la'akari da yawan mahalarta taron, ko shakka babu za a iya cewa taro ne da zai zamo mai matukar girma a tarihi.

Bisa kididdigar da ma'aikatan dandalin tattalin arzikin duniya suka gabatar, an ce tattalin arzikin Afirka ya samu karuwa da ke tsakanin kashi 2 zuwa 3 bisa dari cikin shekaru 25 da suka gabata, inda wannan karuwa ta wuce matsakaiciyyar karuwa da ake samu tsakanin kasashen duniya.

Har ila yau kuma, ana sa ran ganin saurin karuwar tattalin arzikin nahiyar ya kai kashi 4.5% a shekarar nan ta 2015, bisa yadda ake zuba karin jari ga nahiyar, musamman ma a fannin gina kayayyakin more rayuwa, da karuwar amfanin gona da nahiyar ke samu.

A nasa bangare, asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya yi hasashen cewa wasu kasashe 7 daga cikin kasashe 10 mafiya samun karuwar tattalin arziki a shekarar 2015, za su kasance daga yankin kudu da hamadar Sahara, yayin da karuwar tattalin arzikin wannan yanki zai ninka matsakaiciyyar karuwar tattalin arzikin duniya har sau 2.

Dangane da wannan taro da zai zamo karo na 25 da za a gudanar a wannan karo, darakta mai kula da harkokin Afirka na dandalin Elsie Kanza, ya ce yayin taron za a tattauna game da ci gaban da nahiyar Afirka ta samu a fannonin tattalin arziki, da zamantakewar al'umma, da siyasa, tun daga shekarar 1990 ya zuwa wannan lokaci. Sa'an nan, masu ruwa da tsaki za su yi amfani da wannan taro, wajen tattauna dabarun da aka yi amfani da su a baya, da kokarin kirkiro wasu sabbin dabaru, ta yadda za a taimakawa nahiyar warware matsalar da take fuskanta, gami da tinkarar kalubalen da ka iya fuskantar ta a nan gaba.

Sanin kowa ne dai akwai tarin matasa, da ma'aikata 'yan kwadago a nahiyar Afirka, kana an yi hasashen cewa nan da shekaru 30 masu zuwa, cikin duk yara 5 a duniya 1 zai zamo daga nahiyar ta Afirka. Bisa wannan hasashe ne kuma, ya sa dole a fi mai da hankali kan ci gaban harkokin matasan Afirka, da na shugabannin matasan, ta yadda za a samar da wakilcin shugabannin matasan 200, wadanda za su halarci wannan taro.

Batutuwan da za a tattauna za su hada da yadda masu masana'antu a kasashen Afirka za su yi amfani da karin damammaki da ake da su, wajen ci gaba da inganta fasahohi, da habakar kasuwanni, da yadda sabbin shugabannin kasashen Afirka za su yi amfani da boyayyen karfin kasashensu don tinkarar kalubaloli daban daban, da musayar ra'ayin da za a yi tsakanin shugabannin nahiyar 'yan mazan jiya da na yanzu.

Bisa rahotannin 'yan kasuwan kasashen waje masu zuba jari ga nahiyar Afirka, da alkaluman da jaridar "Financial Times" ta kasar Birtaniya ta gabatar, an ce nahiyar Afirka ta riga ta zama wani yankin da ya fi janyo jari a duniya. Inda a shekarar 2014, jarin da aka zuba a nahiyar ya karu da kashi 65%, wanda ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 87. Yayin da yawan fannonin da suka samu jarin 'yan kasuwar kasashen na waje kai tsaye ya karu da kashi 6%.

Bisa la'akari da wannan yanayin da ake ciki, na burin zuba jari ga nahiyar Afirka, ya sa za a tattauna wasu batutuwan da suka jibinci hakan, kamar batun yanayin kasuwar jari a Afirka, da fasahar da za a bi wajen tara kudi, da kokarin da ake yi na shiga fannonin cinikayyar da ake gudanarwa a duk duniya, da dai makamantansu.

Ban da haka kuma, taron zai kara maida hankali ga kasuwar fasahar sadarwa, da wasu sabbin sana'o'i, yayin da ake tattauna wata sabuwar hanyar da za a bi domin raya nahiyar ta Afirka.

Yanzu haka dai cikin ajandar taron, an riga an kebe wasu taruka, inda za a tattauna fasahar wayar salula, da gyare-gyaren da za a iya yi ga shafin yanar gizo na Internet, da yunkurin yayata fasahar zamani, da sabbin fasahohin kafofin watsa labaru, da dai sauransu. Har wa yau kuma, za a kara ba da shawarwari dangane da ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka, musamman ma a fannonin fasahar makamashi mai tsabta, da tattalin arzikin da ya shafi teku, da harkar yawon shakatawa, da dai makamantansu.

Sa'an nan wani bangaren da ya fi janyo hankalin jama'ar duniya shi ne kokarin da kasashen Afirka suke yi, domin tinkarar kalubalolin da suke fuskanta. A wannan bangare, mahalarta taron za su tattauna dangane da hanyoyin da za a bi na warware matsalolin karancin ruwa, da karuwar al'umma, da babban gibin dake tsakanin masu hannu da shuni da matalauta.

Sauran fannonin sun hada da bambancin samar da ilimi, da koma baya a fannin samar da kayayyakin more rayuwa, da rashin kyakkyawar damar samun kulawar lafiya da magunguna, da karancin abinci, da yaduwar bindigogi tsakanin al'umma, da karancin wutar lantarki, da dai sauransu.

Don gane da tattaunawa a fannin fasahar daidaita matsaloli kuwa, ana da fatan kara azama a samun ci gaba mai dorewa a daukacin nahiyar ta Afirka. Ban da wannan kuma, za a tattauna game da batun masu kaura dake ciki da wajen Afirka, da nufin tsara sabbin manufofi a wannan fanni, ta la'akari da yanayin da nahiyar Afirka take ciki, na samun kabilu da yawan su ya kai kimanin 3000, da kuma harsuna da yawansu ya kai kimanin 2000, da ma yadda kabilun nahiyar daban daban suke rikici da juna sakamakon bambancin al'adu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China