in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin kasar Madagascar ta zartas da wani kuduri na tsige shugaban kasar
2015-05-27 10:25:20 cri
Majalisar dokokin kasar Madagascar ta zartas da wani kuduri na yunkurin tsige shugaban kasar Hery Rajaonarimampianina ta hanyar jefa kuri'un yanke kauna. Wata sanarwa da majalisar ta gabatar, ta nuna cewa tuni 'yan majalisu 125 cikin jimillar 'yan majalissa 151 suka jefa kuri'unsu. Kuma 121 sun amincewa da kudurin, sai kuri'u 4 na wadanda ke adawa da hakan. Hakan dai ya nuna cewa kuri'un wadanda suka amincewa da wancan kuduri sun kai kashi 2 cikin 3. Bisa tsarin mulkin kasar ta Madagascar, kotun kolin kasar mai lura da tsarin mulki ce za ta yanke hukuncin karshe game da sakamakon kuri'un da 'yan majalissun suka kada. (Lami)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China