in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Madagascar ta yi murabus
2015-01-14 10:04:06 cri

Faramistan kasar Madagascar, dokta Kolo Roger ya gabatar da takardar murabus dinsa tare da ta gwamnatinsa a ranar Litinin a Antananarivo, babban birnin kasar, a cewar wata sanarwar fadar shugaban kasar Madagascar da aka samu a ranar Talata.

Domin tabbatar da wannan murabus, shugaban Madagascar ya dauki mataki tare da sanya hannu kan wani kudurin tabbatar da hakan. Wannan kuduri, bisa babinsa na farko ya nuna cewa, ana amincewa da murabus din faraminista dokta Kolo Roger da sunansa da kuma sunan gwamnatinsa, a cewar wannan sanarwa.

Haka kuma sanarwar ta nuna cewa, har zuwa lokacin kafa sabuwar gwamnati, mambobin tsofuwar gwamnatin da ta yi murabus ne za su ci gaba da tafiyar da harkokin kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China