in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zazzabi ya hallaka mutane 47 a Madagascar
2014-11-25 10:54:12 cri

Mahukunta a tsibirin Madagascar sun sanar da rasuwar mutane 47, sakamakon kamuwa da wani nau'in zazzabi wanda ke yadawa.

Mai magana da yawun hukumar lafiyar kasar Tafangy Philemon ne ya tabbatar da hakan yayin wani taron manema labarai, biyowa bayan sanarwar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi game da bullar cutar.

A cewar Mr. Philemon, akwai wasu karin mutane 138 da ke dauke da wannan cuta mai asali daga beraye, kuma cutar kan bulla a kasar kusan ko wace shekara, inda adadin wadanda kan kamu da ita ke kasancewa tsakanin mutane 300 zuwa 600, ciki hadda kusan mutane 30 da ke harbuwa da nau'in cutar mai lahanta huhu.

Ya kuma kara da cewa, a ko wace shekara a kalla mutane 10 zuwa 70 na rasuwa sakamakon kamuwa da wannan annoba.

Hukumar lafiya ta WHO dai ta ce, baya ga wadanda cutar ta hallaka a wannan karo, akwai kuma wasu mutanen su 119 da mai yiwuwa su ma sun harbu da kwayoyin cutar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China