in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ravalomanana ya soke halartarsa cikin shirin sassanta 'yan kasar Madagascar
2015-04-15 10:54:40 cri

Tawagar tsohon shugaban tsibirin Madagascar Marc Ravalomanana ta dauki niyyar dakatar da halartarta a cikin shirin sassanta 'yan kasa. Mista Ihanta Randriamandranto, mamba na tawagar, ya bayyana a ranar Litinin cewa, bangaren Ravalomanana ya dauki niyyar janye jiki har sai mun samu karin haske kan sahihiyar manufar da ake baiwa batun sassanta 'yan kasa.

A cikin watan Febrairun da ya gabata, tsoffin shugabannin kasar Zafy Albert da Andry Rajoelina sun sanar da janyewarsu daga shirin sassanta 'yan kasa da kwamitin mabiya addinin kirista (FFKM) ke jagoranta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v An kafa sabuwar gwamnati a Madagascar 2015-01-26 10:42:56
v An nada sabon firaministan Madagascar 2015-01-15 10:30:55
v Gwamnatin Madagascar ta yi murabus 2015-01-14 10:04:06
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China