in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada sabon firaministan Madagascar
2015-01-15 10:30:55 cri

Rahotanni daga Antananarivo ya bayyana cewa, an nada Janar Ravelonarivo Jean a matsayin sabon firaministan kasar Madagascar, kamar yadda babban sakataren fadar shugaban kasa Ralala Roger ya tabbatar a ranar Laraban nan, kwanaki biyu bayan murabus din da Kolo Roger da gwamnatinsa suka yi.

An nada Jean ne bisa doka ta 54 ta kundin tsarin mulkin kasar ta Madagascar wadda ta ba da izinin ga shugaban kasa ya nada firaminista daga cikin sunayen da jam'iyyar siyasar da ta fi rinjaye a majalisar dokokin kasar suka mika, a cewa Rolala lokacin da yake karanta dokar shugaban kasa.

Tsaffin ministoci za su tafiyar da ayyukun yau da kullum na gwamnati har sai sabuwar gwamnati ta fara aiki, in ji shi.

Kolo Roger wanda aka nada shi a watan Afrilun shekara ta 2014 ya mika takardar yin murabus din shi ne ga shugaban kasar Hery Rajaonarimampianina a daren ranar Litinin. A ranar Talata kuma 'yan majalaisar dokokin kasar suka mika sunaye 14 wadanda suke son a zabi daya daga ciki ya zama firaminista.

Jean dai tsohon shugaban klub din Rotary ne a tsibirin mafi girma na tekun India kafin wannan nadin nashi. Ya kuma rike mukamin babban darekta a kamfanin SEIMAD, wanda yake gina gidaje ga ma'aikatan gwamnati lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Didier Ratsiraka. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China