in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu sabon ci gaba wajen hadin gwiwar kasashen Sin da Chile a fannin hada-hadar kudi
2015-05-26 10:54:31 cri

A jiya Litinin,firaministan kasar Sin Li Keqiang wanda ke ziyara a kasar Chile ya bayyana cewa, bayan kammala shawarwari tare da shugabar kasar Michelle Bachelet a fadarta dake birnin Santiago, an samu sabuwar ci gaba wajen yin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin hada-hadar kudi.

Li Keqiang ya bayyana a ganawar sa da manema labaru tare da Shugaba Michelle Bachelet cewa, a lokacin ziyararsa, an samu wannan sabon ci gaba a fannin hadin gwiwar hada-hadar kudi a tsakanin kasashen biyu, wadanda suka kulla yarjejeniyar musayar kudi, an kuma kafa bankin musayar kudin Sin na farko na Latin Amurka a birnin Santiago. Ya ce Kasar Sin ta yi maraba da matakin da kasar Chile ta dauka wajen daina karbar kudin da masu yawon shakatawa na Sin za su biya don neman samun takardar Visa tun daga watan Yuli na wannan shekara.

Kazalika, Li Keqiang ya ce, tattalin arzikin duniya na samun farfadowa sannu a hankali, kuma yana fuskantar yiwuwar ci gaba da lalacewa. Bisa wannan yanayin da ake ciki ne, kokarin inganta hadin gwiwar kasashen biyu a fannin hada-hadar kudi, da buga haraji, da karfin samar da kayayyaki, zai sanya a kara zuba wa juna jari da kuma bunkasa tattalin arzikin bangarorin 2, ta yadda za su ba da gundummawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

A nata bangare, Michelle Bachelet ta ce, an samu karin zarafi wajen hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, don haka kasar ta na kokari tare da kasar Sin, don kara imani da juna, da karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da hada-hadar kudi, da kara zuba jari ga juna, da kuma kara yin cudanya tsakanin jama'arsu, domin raya huldarsu cikin sauri.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China