Firaministan kasar Sin Li Keqiang da shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff sun gana da manema labaru tare bayan da suka yi shawarwari a jiya Talata da safe a birnin Brasilia.
A jawabinsa Li Keqiang ya nanata cewa, a yayin da ake fuskantar matsin lamba sosai a fannin farfado da tattalin arzikin duniya, a matsayinsu na muhimman kasashe da tattalin arzikinsu ke samun ci gaba cikin sauri, kara hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Brazil zai karfafa gwiwar kasashe masu tasowa, kuma zai ba da gundummawa ga yunkurin da ake na farfado da tattalin arzikin duniya.
A nata bangare, Dilma Rousseff ta ce, kasashen Brazil da Sin za su ci gaba da yin hadin gwiwa a MDD da kungiyar G20 da kungiyar kasashen BRICS, domin kara taka rawa kan harkokin kasa da kasa da na yankuna daban daban na duniya.(Lami)