in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya duba na'urorin kasar Sin da ake nuna wa a kasar Brazil
2015-05-21 09:12:12 cri

A jiya Laraba da safe ne a birnin Rio De Janeiro na kasar Brazil, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada a yayin da yake kallon jiragen kasa na karkashin kasa da kasar Sin ta kera cewa, ya kamata a zurfafa hadin gwiwar kawo moriyar juna da kara inganta na'urorin da kasar Sin ta kera. Ya kuma ziyarci na'urorin kasar Sin da aka baje kolin su.

Kazalika, Mr. Li Keqiang ya ce, cimma nasarar yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Brazil wajen kera jiragen kasa dake tafiya a karkashin kasa ya shaida cewa, kasar Sin na da kwarewa sosai a fannin kera jiragen kasa da layin dogo masu inganci da kuma araha,wadanda kuma ke biyan bukatun kasashe daban daban na duniya.

Kasar Sin tana son ci gaba da karfafa hadin gwiwa tare da kasar Brazil a fannin gina kayayyakin more rayuwa da kera na'urori, domin habaka hadin gwiwarsu yadda ya kamata.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China