in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi kira da a kawo karshen rikicin kasar Sham
2015-03-13 10:52:30 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya sake jaddada kira ga daukacin sassan masu ruwa da tsaki, da suka gaggauta daukar matakan shawo kan rikicin siyasa dake addabar kasar Sham.

Kaza lika ya bukaci kasashen duniya da su kara goyon bayan su ga kudurin MDD na warware matsalar kasar ta Sham ta hanyar siyasa.

Ban Ki-Moon wanda ya gabatar da wannan bukata cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a jiya Alhamis, ya ce an kwashe shekaru biyar ke nan gwaza fada a kasar Sham, lamarin da ya janyo rasuwar mutane dubu 220, tare da tilastawa dubban al'ummar kasar kauracewa gidajensu, ciki hadda wasu kimanin miliyan 4, da suka tsallaka zuwa kasashe makwabta domin kaucewa rikicin, yayin da mutane miliyan 7.6 suka zama 'yan gudun hijira.

Ban Ki-Moon ya kara da cewa, a yanzu haka kasashe daban daban na dora muhimmanci kan kalubalen da kungiyar IS, da sauran kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi ke haifarwa ga al'umma, sai dai a cewarsa magance rikicin kasar Sham, zai taimaka wajen ganin bayan masu tsattsauran ra'ayi dake bazuwa ko ina a yankin.

Bugu da kari, Ban Ki-Moon ya ce daidaita rikicin kasar Sham ta hanyar siyasa na da muhimmancin gaske. Don haka ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Sham, da su dakatar da tashe-tashen hankula, tare da komawa teburin shawarwari. A daya hannun kuma Mr. Ban ya yi kira ga kwamitin sulhun MDD, da ya dauki managartan matakai na kawo karshen rikicin kasar ta Sham.

A wani ci gaban kuma, asusun yara na MDD ya ce tashe-tashen hankula dake faruwa a kasashen Sham da Iraki, sun yi mummunan tasiri ga yara da matasa kusan miliyan 14 a kasashen su. Don haka Asusun ya yi kira ga kasashen duniya da su samar wa wadannan rukuni damar samun tarbiyya, da tausayawa, tare da ba su taimakon jin kai. Asusun ya kuma bukaci tallafawa yaran a fannin karfafa aikin samar musu da ilimi, da kafa tsarin kiwon lafiya a yankunan da 'yan gudun hijira ke zaune. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China