in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta nemi sulhu da gwamnatin Sham, in ji Kerry
2015-03-16 10:10:20 cri

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya sanar cewa, Amurka dai za ta nemi sulhu tsakaninta da gwamnatin kasar Sham a kokarin da take na ganin an kawo karshen tashin hankalin da ake a kasar har tsawon shekaru 4.

John Kerry, a hirar da ya yi da talabijin din CBS dake tattaunawa a kan shekaru 4 da fara tashin hankalin kasar Sham da aka watsa ranar Lahadin nan, ya ce, a karshe dai dole su nemi sulhu, domin dama tun tuni Amurka ta nemi a sulhunta bisa yarjejeniyar Geneva ta farko.

Tattaunawar Geneva da aka yi har zagaye biyu a watan Yunin shekara ta 2012 da kuma Janairun shekara ta 2014 duk sun ci tura wajen kawo karshen fadan kasar ta Sham, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 220,000, fiye da rabin mazauna kasar kuma aka tilasta musu tserewa daga gidajensu domin neman tsirar da ransu, yanzu haka kuma kusan al'umma miliyan 4 na gudun hijira a sansanonin 'yan gudun hijira dake kasashe makwabta.

John Kerry ya dora laifin rashin mai da hankali a kan yarjejeniyar kan shugaban kasar ta Sham Bashar al-Assad wanda ya sa duka yarjejeniyar suka ci tura. Yana mai bayanin cewa, yanzu haka dai Amurka na kokari tare da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an sake cimma wata mafita ta diplomasiyya, domin kowa ya amince cewa, ba za'a cimma mafita da karfin soja ba, sai da a siyasance.

Shirin gwamnatin Obama a kan Sham yana zuwa ne sakamakon karin tsananta bincike a gida da waje, ganin yadda a baya ya nace cewa, saukar da Assad ne kadai mafita ta sulhunta batun kasar Sham, sai kuma yanzu ya yi shiru tun bayan da kasar ta kai hari a kan 'yan kungiyar IS a kasashen Iraqi da Sham a shekarar bara. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China