in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin da shugaban kasar Columbia sun yi ganawa
2015-05-22 11:36:50 cri
Firaministan kasar Sin Mista Li Keqiang, wanda ke ziyarar aiki a kasar Columbia, ya gana da shugaban kasar Juan Santos Calderón, a yammacin ranar Alhamis.

Yayin zantawar tasu, firaministan kasar ta Sin ya isar da gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaba Santos, tare da jajantawa game da rasuwar wasu 'yan kasar, sakamakon zabtarewar kasa da ta auku a arewacin kasar ta Columbia.

A cewar Mista Li Keqiang, tsare-tsaren tattalin arzikin kasashen Sin da Columbia na iya biyan bukatun junansu, don haka akwai fannoni da yawa da kasashen 2 za su iya hadin gwiwa cikinsu. Kana kasar Sin na fatan ganin bangarorin 2 sun kara zubawa juna jari, da inganta hadin gwiwa a fannonin sana'o'i daban daban.

A cewar firaministan, za a fi mai da hankali kan hadin kan sassan biyu a bangaren bunkasa masana'antu, da samar da na'urori. Haka zalika ana maraba da shigowar kamfanonin kasashe masu sukuni, cikin hadin gwiwar kasashen 2, a matsayin wani bangare na 3, ta yadda za a taimakawa raya masana'antu a kasar ta Columbia.

Firaministan ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin tana sa kaimi ga kamfanonin kasar, wajen shiga aikin raya ababen more rayuwa a Columbia, musamman ma a fannonin ginin hanyoyin mota, da layin dogo na karkashin kasa, da tashar jiragen ruwa, da dai sauransu.

A nashi bangare, shugaba Santos na kasar Columbia ya yi maraba da zuwan firaminista Li Keqing, tare da jinjinawa yadda kasashen 2 ke yaukaka huldarsu a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu, tun bayan kulla huldar diplomasiyya shekaru 35 da suka gabata. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China