in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya fara ziyarar aiki a kasar Columbia
2015-05-22 08:01:30 cri
Bisa gayyatar da shugaban kasar Columbia Juan Manuel Santos ya yi masa, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa birnin Bogota, fadar mulkin kasar Columbia, a ranar Alhamis 21 ga watan nan, domin fara ziyarar aiki a kasar.

Ministar harkokin wajen kasar Madam Maria Holguin ce ta tarbi mista Li a filin jirgin saman kasar, inda sojojin kasar suka yi masa faretin girmamawa.

Jim kadan da saukarsa, Mr. Li wanda ya samu rakiyar uwar gidansa da sauran mukarraban gwamnati, ya bayyana cewa kasar Columbia, wata muhimmiyar kasa ce a nahiyar Latin Amurka. Kuma a shekarun baya bayan nan, huldar dake tsakanin Sin da Columbia ta kai ga wani sabon matsayi, inda a yanzu haka ake fuskantar sabbin damammaki, tare da samun ci gaba cikin sauri, ta fuskar hadin gwiwar sassan biyu a fannoni daban daban.

Firaminista Li ya kara da cewa, zuwansa Columbia a daidai lokacin da ake murnar cika shekaru 35 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da kasar, na nuni ga burin zurfafa zumunci tsakanin bangarorin 2, da karfafa hadi gwiwarsu a fannonin samar da ababen more rayuwa, da samar da na'urori, da bunkasa aikin gona da dai sauransu, ta yadda hakan zai inganta manufar shimfida zaman lafiya a kasar ta Columbia, da ci gaban tattalin arzikinta, da bunkasa zamantakewar al'ummar kasashen 2. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China