in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Peru sun gana da manema labaru
2015-05-23 17:07:57 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, da shugaban kasar Peru Ollanta Humala Tasso sun gana da manema labaru tare a yammacin ranar Jumma'ar da ta gabata, bayan da suka yi shawarwari a birnin Lima.

A yayin taron manema labarun, firaminista Li ya yi bayani kan sakamakon da suka samu a gun shawarwarin nasu, ya kuma bayyana cewa, kasar Peru zango na uku ne a wannan ziyararsa a kasashen Latin Amurka guda hudu. Kazalika ya nuna cewa, kasar Sin ta samu fasahohi masu yawan gaske a fannin gina hanyar dogo, na'urorinta ma suna da fifiko ta fuskar inganci da farashi, wadanda suka ci jarrabawa a kasuwar duniya. Bayan haka kuma, kasar Sin na sa himma wajen shiga ayyukan gina hanyar dogo tsakanin tekun Pasific da Atlantic, wadda ta ratsa nahiyar Amurka ta kudu,, da kuma sauran ayyukan gina hanyoyin jiragen kasa a yankin. Kana a yayin da take gudanar da hadin kai a fannin na'urori a tsakaninta da kasashen Latin Amurka, a sa'i guda tana kokarin karfafa musayar fasahohi, da nufin taimakawa kasashen dake yankin wajen yin mu'ammala da juna, da inganta bunkasuwar tattalin arzikin yankin, ta yadda za su iya tabbatar da samun moriyar juna da samu nasara tare.

A nasa bangaren ma, shugaba Ollanta Humala Tasso ya bayyana cewa, kasarsa na fatan kara hadin kai a tsakaninta da kasar Sin, tana kuma yin godiya ga kasar Sin kan jerin shawarwarin da ta gabatar game da raya masana'antun kasar Peru, kasar kuma na maraba da Sin da ta kara zuba jari a kasar ta fannonin hakar ma'adinai, da sha'anin noma da dai sauransu. Shugaban ya kuma bayyana cewa, takardar bayani da kasashen biyu suka cimma game da nazarin yiwuwar gina hanyar dogo tsakanin tekun Pasific da Atlantic, ya inganta da kuma karfafa dangantakar hadin kai na sada zumunta a tsakanin kasashen biyu, wanda zai taimaka wa kasar Peru wajen tabbatar da samun ci gaba, har ma da inganta samun bunkasuwa da wadata tare a tsakanin kasashen Peru, da Brazil, da kuma Sin.

Bisa gayyatar da shugaban kasar Peru Ollanta Humala Tasso ya yi masa ne, a ranar 22 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang tare da uwargidansa Cheng Hong suka soma ziyarar aiki a kasar, bayan da suka kammala ziyara a kasar Columbia. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China