in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gabatar da sabon salon raya hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen kudancin Amurka
2015-05-20 15:42:50 cri

Firaministan Sin Li Keqiang ya halarci taron kolin masana'antun kasashen Sin da Brazil, tare da shugabar Brazil Dilma Rousseff, gami da gabatar da jawabi a wajen. Yayin taron na jiya Talata, Mr. Li ya gabatar da sabon salon raya hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen dake yankin kudancin Amurka.

Ya ce, na farko akwai bukatar kara biyan bukatun kasashen kudancin Amurka, wato a raya hadin gwiwar sufurin kayayyaki, da samar da wutar lantarki, da inganta harkokin sadarwa, don cimma burin kara cundayar kasashen dake nahiyar.

Sannan kuma, a bi dokokin tattalin arziki da kasuwanni, don kara samun hadin gwiwar masana'antu, da zamantakewa tsakanin gwamnatoci na kasashen da abin ya shafa. A karshe kuma, a inganta hadin gwiwa tsakanin sassan a fannonin tattara kudade, kamar kafa asusun, da samar da rance, da ba da inshora.

A nata bangare, shugaba Rousseff ta ce, Brazil tana maraba da masana'antun Sin a fannin shiga ayyukan samar da wutar lantarki, da gina hanyoyin jiragen kasa na kasar. Kaza lika, tana kuma sa ran kara yalwata cinikayyar kasashen biyu, don samun damar raya cinikayya daga dukkanin fannoni, da karfafa hadin gwiwa a fannin hada-hadar kudi, ta yadda hakan zai kara inganta hadin gwiwar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi, don kawo alheri ga kasashen da jama'arsu. Ta ce, ta hakan ne, za a farfado da tattalin arzikin duniya yadda ya kamata. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China