in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a kawo karshen gwajin makaman nukuliya
2014-09-11 14:47:43 cri

Babban sakatare na MDD, Ban Ki-moon da kuma shugaban babban taron majalisar, John Ashe, sun yi kira a ranar Laraba da a sake daukar niyya ta samun wata duniyar da babu makaman nukuliya da gwaje-gwajen nukuliya, tare da nuna cewa, an gudanar da gwaje-gwajen nukuliya kusan 2000 tun daga bakin shekarar 1945.

Fatanmu na wata duniyar da babu makaman nukuliya, shi ne na ganin hakan ya bayyana bisa niyyarmu ba tare da kasala ba domin hana gwaje-gwajen makaman nukuliya, in ji John Ashe, a cikin wani sakon da mataimakin babban taron MDD, Charles Thembani Ntwaagae ya karanta, a yayin wani taron da ba na hukumance ba domin karrama ranar kasa da kasa ta yaki da gwaje-gwajen makaman nukuliya.

Gwajin makamai, kamar yin wasa da wuta ne, in ji wani karin magana, shi ne kai kan mu bisa hanyar da muke fatan mu kaucewa, kana kuma shi ne na janyo babbar illa ga muhalli da lafiyar jama'a.

Da ake bikinta a ko wace shekara a ranar 29 ga watan Agusta, wannan rana na da manufar janyo hankalin MDD, kasashe mambobi da kungiyoyi masu zaman kansu kan wajabcin hana gwaje-gwajen makaman nukuliya.

A nasa bangare, Ban Ki-moon ya tunani kan ziyarar da ya kai a cikin watan Afrilun shekarar 2010 a Semipalatinsk, wata tashar nukuliya da kasar Kazakhstan ta rufe a shekarar 2009, kana kuma ya kara da cewa, gwaje-gwajen da aka gudanar a wannan wurin da kuma sauran wurare a wasu kasashen duniya bayan yakin duniya na biyu sun zama gwaje-gwaje na manufar mallakar makaman nukuliya.

Haka kuma Ban Ki-moon ya nuna damuwa cewa, yarjejeniyar hana gwaje-gwajen makaman nukuliya (TICEN) da babban taron majalisar ya cimma yau da kusan shekaru 18 da suka wuce, ba ta fara aiki ba har yanzu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China