Shugaba Nkurunziza ya ce, sun samu labarin harin da kungiyar Al-shabaab ke shirin kaiwa Burundi, wadda ta tura sojoji zuwa tawagar musamman ta AU dake Somaliya. Yana mai cewa, ya kamata kasar ta yi hattara game da harin ta'addanci da za a kawo. Baya ga wannan kuma, a cewarsa, ya riga ya tattauna wannan batu tare da mahukuntan kasashen Kenya da Uganda wadanda su ma suka tura sojoji ga tawagar AU a Somaliya.
Bisa labarin da gidan rediyon kasar Burundi ya bayar a ranar 15 ga wata, an ce, yunkurin kifar da gwamnatin da Niyombare ya jagoranta bai yi nasara ba.
Rahotanni na cewa, a ranar 16 ga wata, an gurfanar da mutane 18 da aka kama da hannu a shirin juyin mulkin gaban kuriya, amma har yanzu, ba a san inda Niyombare yake ba.(Bako)