Shugaba Nkurunziza, ya kuma bukaci al'ummar kasar ta Burundi da su kaucewa daukar duk wasu matakai na ta da hankali da keta dokokin kasar. Daga nan sai ya bukaci ma'aikatar kudin kasar da ta samar da alkaluman kudade da za a bukaci domin cimma nasarar shirya zaben.
Ya ce akwai bukatar daukacin kasashen duniya su ci gaba da marawa kasarsa baya, game da zaben da ake shirin gudanarwa, domin kaucewa duk wani yanayi maras kyau da ba a fata.
A wani ci gaban kuma, babban magatakardar MDD Ban Ki Moon, ya ja hankalin shuwagabannin yankin gabashin Afirka, da su yi hadin gwiwa wajen warware matsalar siyasar dake addabar kasar Burundi. Mr. Ban ya bayyana wannan shawara ne yayin wata zantawar da ya yi da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ta wayar tarho.
A jiya Jumma'a ma dai kwamitin tsaron MDD ya bayyana matukar damuwarsa, game da halin da ake ciki a Burundi, biyowa bayan yunkurin juyin mulkin soji da bai yi nasara ba. Kwamitin ya kuma bayyana muhimmancin tattaunawa tsakanin sassan kasar, ta yadda za a iya kaiwa ga warware matsalolin kasar cikin lumana da kwanciyar hankali. (Saminu Hassan)