in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Burundi ya bayyana a karon farko tun bayan yunkurin juyin mulki
2015-05-17 20:34:08 cri
Shugaba Pierre Nkurunziza na kasar Burundi, ya bayyana a karon farko, tun bayan yunkurin juyin mulkin soji da bai yi nasara ba. Nukurunziza wanda ya gana da 'yan jaridu a Lahadin nan, a fadar sa dake birin Bujumbura, ya yi tsokaci game da kalubalen tsaro da ake fuskanta a shiyyar, sai dai bai ce kome ba game da halin siyasar kasar.

Kaza lika ya bayyana ra'ayin sa game da barazanar da kungiyar Al- Shabaab ke yiwa dukkanin kasashen da suka shiga shirin kungiyar AU, na tallafawa yakin da ake yi da kungiyar a Somalia, ciki hadda ita kan ta Burundi.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai shugaba Nkurunziza ya yi kira ga daukacin al'ummar kasar ta sa, da su marawa shirin gudanar babban zaben kasar dake tafe baya, su kuma kauracewa tada husuma.

Gabanin hakan, a ranar Laraba tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar ta Burundi, ya sanar da hambarar da shugabancin gwamnatin kasar mai ci, lokacin da shugaban kasar ke halartar wani taro a Tanzania. Kafin daga bisani dakarun gwamnatin kasar su shelanta murkushe yunkurin juyin mulkin, bayan gabza wani kazamin fada a birnin Bujumbura.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China