in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya isa kasar Brazil
2015-05-19 11:04:09 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya isa kasar Brazil a jiya Litinin, domin fara ziyarar aiki bisa gayyatar shugaba Dilma Rousseff.

Cikin jawabin da ya gabatar jim kadan da saukarsa, Mr. Li ya ce. hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasar Brazil, na cike da ma'ana, matakin da kuma ke dada bunkasa kawancen kasashe masu tasowa, tare da karfafa tsarin tattalin arzikin kasashen, da ma bunkasa sha'anin rayuwar al'ummunsu.

Mr. Li ya ce, kasarsa na fatan zurfafa musaya da mahukuntan kasar Brazil, a fannomin amincewa juna ta fuskar siyasa, da fadada hadin kai, tare da musayar al'adu, da bunkasa sha'anin samar da kayayyaki, da kara inganta masana'antun kirar na'urori, da sha'anin samar da ababen more rayuwa, da cinikayya, da kuma fannin zuba jari.

Firaministan kasar ta Sin ya kara da cewa, zai tattauna da mahukuntan kasar Brazil game da batutuwan da suka shafi hadin gwiwar kungiyar BRICS, da batun canjin yanayi, da hadin gwiwar kasa da kasa a fannin hada hadar kudade, da kuma batun hadin gwiwar Sin da kasashen Latin Amurka, duka dai da nufin bunkasa cimma moriyar juna, da inganta tattalin arziki da kasuwannin kasashe masu tasowa.

Ana dai sa ran yayin wannan ziyara, Mr. Li zai zanta da shugaba Rousseff ta Barazil, kana za su gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa. Kaza lika shugabannin biyu za su ganewa idanunsu, kasaitaccen bikin da za a hada ta kafar talabijin, game da bude tashar samar da lantarki ta ruwa dake Belo Monte, a kasar ta Brazil. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China