Wata sanarwa da hedkwatar tsaron ta fitar a jiya Asabar, ta ce sojojin sun ceto yara kanana da mata a kalla 20, biyowa bayan simamen da suka kai wasu sansanonin kungiyar a ranar Jumma'a. Sanarwar ta kara da cewa duk da kalubalen da sojojin ke fuskanta na tarin nakiyoyi dake binne a sassan dajin, sojojin gwamnatin sun samu nasarar fatattakar 'yan Boko Haram, tare da kwace makamai da dama, da kuma ababen hawa da suke amfani da su.
Sai dai a hannu guda sanarwar ta bayyana rasuwar soja daya, tare da jikkatar wasu sojojin su 10, sakamakon fashewar nakiyoyi, yayin da suke kutsawa cikin dajin na Sambisa, baya ga kuma na'urori, da motocin sojojin da suka lalace sakamakon hakan.
A wani ci gaban kuma, sojojin Najeriyar na ci gaba da binciken kwakwaf a kauyen Bitta dake jihar ta Borno, bayan da wani gurneti da wasu yara biyu suka cinta a wani juji ya tashi ya kuma raunata yaran. Ana dai zaton wani dan kunar bakin wake ne ya jefar da gurnetin, lokacin da yake yunkurin tserewa daga kauyen, wanda ke makwaftaka da dajin na Sambisa. (Saminu Hassan)