An dage taron Malabo kan kungiyar Boko Haram
Taron gaggawa na shugabannin kasashen yammacin Afrika da na yankin tsakiya, da aka tsaida shirya wa a ranar 18 ga watan Afrilu a birnin Malabo na kasar Guinee Equatoriale domin tattauna batun kungiyar masu kaifin kishin islama ta Boko Haram da ke Najeriya, an dage shi a cewar wani jami'in ma'aikatar sadarwa ta kasar Guinee Equatoriale a ranar Asabar. Taron da zai tattara shugabannin kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika (ECOWAS) da kuma gamayyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika (CEEAC), za'a gudanar da shi a gaba, bayan kama aikin sabon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, a cewar wannan majiya. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku