Sakatare janar ya kadu sosai da cigaba da sace sacen kananan yara da amfanin da ake da su a baya bayan nan a matsayin 'yan kunar bakin wake, haka kuma tare da bayanan da ake samu masu nuna cewa yawancin 'yan mata da mata da Boko Haram ke tsare dasu an yi musu fyade sau da dama a lokacin da aka kama su da kuma tilasta musu auren dole tare da mayakan Boko Haram bisa tsarin kamfen tsare mutane dole da yiwa mata fyade, in ji kakakin Ban Ki-moon a cikin wata sanarwa.
Masu hannu kan wadannan munanan ayyuka ya kamata a bayyanar da su gaban kuliya, in ji kakakin tare da yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara karfafa samar da kayayyaki na taimakon kiwon lafiya da na kwantar da zukatan wadanda suka tsira.
A cewar sanarwar, mista Ban ya kuma nuna damuwarsa game da 'yan gudun hijira kimanin dubu 40 a kasashen Kamaru, Chadi, Nijar da Najeriya a tsawon makwanni uku na baya bayan nan. Haka kuma yana kira ga mambobin kwamitin tafkin Chadi da kasar Benin dasu kara karfin gamayyar sojojin hadaka na MNJTF da kuma samar da yanayi mai kyau domin dawowar mutanen da ke bukata, sake tsugunar da mutane da dunkulewar mutanen da suka bar muhallinsu da 'yan gudun hijira. (Maman Ada)