Rahotanni sun nuna cewa tun a ranar Laraba dubban jama'ar wannan yanki suka isa kan iyakar Najeriya da Nijar, kafin a daga bisani a tara su a wani sansanin 'yan gudun hijira dake garin Geidam, a jihar Yoben Najeriya.
Da yake tsokaci game da hakan, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce tun da farko mahukuntan kasar Nijar sun umarci al'ummun tsibirin da su fice daga yankin ne, sakamakon matakin soji da ake shirin dauka kan mayakan Boko Haram, wadanda suka mamaye yankin.
A cewar gwamnan jihar Diffa, gwamnatin Nijar ta umarci jama'ar yankunan da fice daga yankunan na su ne, bayan da mayakan Boko Haram suka hallaka mutane da dama dake zaune a yankunan a karshen watan da ya gabata.
A baya bayan nan ma dai dakarun kungiyar ta Boko Haram sun hallaka wasu mutane 5, yayin wani farkami da su kaddamar a kauyen Koukodou, dake yankin Dosso a kudu maso yammacin kasar ta Nijar. (Saminu)