Kakakin rundunar sojin Najeriya Kanar Sani Usman ne ya tabbatar da hakan, koda yake bai tabbatar da adadin jiga-jigan mayakan kungiyar da sojojin suka kashe ba. Amma ya ce, da dama daga cikinsu an harbe su ne yayin da sojojin ke kokarin tarwatsa sansanin samun horon kungiyar da ke dajin na Sambisa.
Bugu da kari kakakin rundunar ya shaidawa Xinhua cewa, sojojin sun kara ceto mata da kananan yara baya ga mata 300 da aka ceto a baya a dajin.
Kwararru kan harkar tsaro a Najeriya na cewa, yaki da ta'addancin da Najeriya ke aiwatarwa a yankin arewa maso gabashin kasar na haifar da sakamako mai kyau, ganin irin nasarorin da dakarun ke samu kan mayakan na Boko Haram. (Ibrahim)