in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya tashi zuwa Brazil
2015-05-17 16:49:18 cri
A safiyar yau Lahadi 17 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya tashi zuwa birnin Brasilia, fadar mulkin kasar Brazil, domin gudanar da ziyarar aiki a karo na farko, a nahiyar Latin Amurka da yankin Caribbean.

Bisa goron gayyatar shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff, da takwaransa na Columbia, Juan Manuel Santos Calderón, da na Peru, Ollanta Moisés Humala Tasso, da kuma takwaransa na kasar Chile, Michelle Bachelet, firaministan kasar Sin Li Keqiang zai ziyarci wadannan kasashe hudu tun daga yau din nan.

Duk dai da nisan dake tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka, sassan biyu sun kasance aminai cikin wani tsahon lokaci. Kana akwai dankon zumunci mai karfi tsakaninsu, baya ga kasancewar bukatun su na kama da juna a fannonin siyasa, da batun neman samun bunkasuwa.

Dadin dadawa, bangarorin biyu na iya taimakawa juna a fannin cinikayya. Don haka dangantaka, da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka ke dada samun tagomashi.

Bugu da kari, a wannan gaba da Sin ke ta kokarin raya tattalin arzikin ta, a hannu guda kuma saurin bunkasar tattalin arzikin yankin Latin Amurka ke raguwa, manazarta na ganin matakan kyautata tsarin tattalin arziki da Sin ke dauka, za su ba da taimako wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu. Don haka ziyarar firaminista Li za ta tabbatar da hadin gwiwar bangarorin biyu, tare da lalubo hanyoyin fadada ci gaba, da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China