Jami'an harkokin wajen EU, Amurka da Switzerland sun bayyana hakan ne a ranar litinin din nan yayin da suke yin shawarwarin siyasa tare da gwamnatin kasar Burundi.
Babban jami'i mai daidaitawa nan kungiyar EU dake yankin babban tafkin nahiyar Afrika, Koen Vervaeke ya bayyana cewa, yanzu kasar halin da ake ciki a Burundi ba ta da wajababbun sharudan shirya babban zaben,bai dace da gudanar da zaben shugaban kasar ba, don haka yana fatan gwamnatin kasar za ta dauki matakai cikin gaggawa, a kokarin don tabbatar da yin gudanar da zaben cikin lumana da adalci. Koen Vervaeke ya kuma yi gargadin cewa, Idan idan kasar ba ta yi haka ba, to kungiyar EU ba za ta ba da sauran kudin tallafin shirya zaben da yawansa ya kai kudin Euro miliyan 2 badon gudanar da zaben kasar ba wato kudin Euro miliyan 2 ba.
Shi ma Jakadan kasar Amurka dake kasar Burundi Dawn Liberi ya bayyana cewa, yanzu jama'ar 'yan kasar Burundi fiye da dubu 10 sun tsere zuwa kasashe makwabta don gudun hijiraka, abin da yasa Amurka ta ke Allah wadai da dukkan irin rikici, kana ta bukaci gwamnatin kasar Burundi da ta amince da yin zanga-zanga cikin lumana. (Zainab)