in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An janye ma'aikata 404 na kamfanin CNPC na kasar Sin daga kasar Sudan ta kudu a sakamakon yaki
2015-05-22 10:41:52 cri

A yayin da wasu ma'aikatan kamfanin man fetur da iskar gas na kasar Sin wato CNPC suka isa birnin Juba, babban birnin kasar Sudan ta kudu a jiya Alhamis, wasu ma'aikata 404 kuma sun bar jihar Upper Nile da ake musayar wuta lami lafiya.

A ranar 19 ga wannan wata ne, dakarun adawa na kasar Sudan ta kudu suka fara kai hari garin Melut na jihar Upper Nile, inda suka yi musayar wuta da sojojin gwamnati a wata masana'antar tace mai, daga bisani yakin ya bazu zuwa yankin Paloch da kamfanin CNPC ke aikin hako man fetur dake da nisan kilomita 20 ko fiye, kana yankin hako man fetur mafi girma na kasar Sudan ta kudu, yawan man fetur da aka hako daga yankin ya kai kashi 80 cikin dari na yawan man fetur da aka hako a kasar Sudan ta kudu.

A halin yanzu, gwamnatin kasar Sudan ta kudu ta kara tura sojoji zuwa yankin domin kare shi. Baya da ma'aikata 404 na kasar Sin da suka janye daga yankin, akwai wasu ma'aikatan da ke ci gaba da kula da muhimman ayyuka a wurin.

Wadannan ma'aikata za su tabbatar da ayyukan samar da man fetur bisa sharadin za a kare rayukansu, amma idan suna bukata za su daidaita na'urori su bar wurin don tsira da rayukansu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China