in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta sake jaddada aniyar aiki da IGAD don magance rikicin Sudan ta Kudu
2015-05-14 10:23:56 cri

Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta ce, tana kara jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki tare da kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka IGAD domin samar da mafita a rikicin da ke ta ci gaba a kasar Sudan ta Kudu.

A cikin sanarwarta ta baya bayan nan game da yanayin da ake ciki a jaririyar kasar, Madam Nkosazana Dlamini Zuma, shugaban kwamitin kungiyar ta lura da cewa, yanayin da ake ciki a Sudan ta Kudu yana nan cikin dar dar babu sauyi.

A cikin sanarwar, kungiyar ta AU ta ce, a makonni 3 da suka gabata, ana ta ci gaba da arangama tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan adawa SPLM a yankin Upper Nile.

Madam Nkosazana Zuma ta ce, yana da muhimmanci a yi kokarin kafa takunkumi a kan duk wadanda suke ta kokarin hana wanzar da zaman lafiya, da kuma saba wa ka'idojin duniya na dokokin jin kai, sannan suke tada zaune tsaye na lalata ayyukan wanzar da zaman lafiya da yanzu haka ake aiwatarwa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China