in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kara nuna damuwa game da halin jin kai a Sudan ta Kudu
2015-05-11 10:27:59 cri

An nuna damuwa game da halin jin kai da al'umma za su fada a kasar Sudan ta Kudu sakamakon janyewar kungiyoyin ba da agajin jin kai da dama saboda yadda fada tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan tawaye ke kara kazanta.

Kungiyar likitocin da babu kan iyaka wato MSF, da kungiyar bayar da agaji ta Red Cross, kowanensu a ranar Asabar din da ta gabata sun bayyana cewa, sun janye ma'aikatansu daga garin Leer na jihar Unity saboda kazamin fadan da ake yi, suna masu bayyana cewa, da dama mutane na fuskantar harin makamai baya ga karancin abinci, ruwan sha da kayayyakin kiwon lafiya.

A cewar MDD, kusan mutane 100,000 a Sudan ta Kudu aka tayar daga muhallansu sakamakon kazamin fadan da ya barke makon da ya gabata.

Kungiyar 'yan tawayen karkashin shugabancin tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, a ranar Lahadin nan ta sanar da cewa, sojojin gwamnati cikin dabara tana kai wa fararen hula hari a wuraren da 'yan tawayen ke da rinjaye domin tilasta su neman mafaka a wajen kasar.

A wani bangaren kuma kakakin sojin kasar Sudan ta Kudu Philip Aguer a ranar Lahadin ya tabbatar da cewa, an yi dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan tawaye a jihar Unity.

Kasar Sudan ta Kudu dai wadda ta samu 'yancin kanta a shekara ta 2011 ta fada cikin rikici ne a watan Disambar shekarar 2013, lokacin da fada ya barke tsakanin sojoji masu biyayya ga shugaba Salva Kiir Mayardit da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China