in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi allah wadai da tashin hankalin da ke faruwa a Sudan ta Kudu
2015-05-21 09:33:42 cri

Babban sakataren MDD BanKi-moon ya yi kakkausar suka kan tashin hankalin da ke faruwa tsakanin dakarun kwatar 'yancin Sudan (SPLM) da abokan adawarsu na SPLA da ke Sudan ta Kudu yau sama da kwanaki 10.

Kakakin MDD ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai cewa, babban sakataren MDD ya bayyana rashin jin dadinsa kan rahotannin keta hakkin bil-adama da bangarorin biyu ke aikata wa, ciki har da kona kauyuka da kisa da yiwa fararen hula fyade a lokacin da suke daukar matakan soja a jihar Unity.

Asusun tallafawa yara na MDD (UNICEF) ya bayyana cewa, tun lokacin da fada ya barke a Sudan ta Kudu shekaru biyu da suka gabata, al'amura sai ci gaba da tabarbarewa suka yi, ganin yadda a jihar Unity ake kashe yara ko yi musu fyade a cikin makonni biyun da suka gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China