in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNMISS na nuna damuwa da sabbin tashe-tashen hankula a Sudan ta Kudu
2015-05-19 09:40:21 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD mai aiki a Sudan ta Kudu UNMISS ta bayyana matukar damuwa, game da barkewar sabbin tashe-tashen hankula a kasar.

Kakakin MDD Farhan Haq ne ya bayyawa taron manema labaru hakan, yana mai cewa, rahotanni daga jihar Upper Nile, na bayyana yadda dakarun 'yan adawar Malakal suka gwabza kazamin fada da sojojin gwamnati. Lamarin da ya jefa dubban fararen hula cikin mawuyacin hali.

Tawagar ta UNMISS dai ta damu matuka bisa kalubalen jin kai da ake fuskanta a Sudan ta Kudu, kasar da ta sha fama da rikice-rikice kusan duk tsahon shekarar bara. Kaza lika UNMISS ta yi Allah wadai da karya yarjejeniyar dakatar da bude wuta, wadda bangarorin kasar suka rattabawa hannu.

An rawaito jami'in tsare-tsare, na hukumar kula da ayyukan jin kai ta MDD a kasar Toby Lanzer, na cewa, fadan da ya kaure a karshen mako kusa da sansanin MDD a jihar Upper Nile, ya raunata fararen hula. Har wa yau akwai rahotannin aikata muggan laifuka da suka hada da fyade, da kisan fararen hula, ciki hadda yara kanana.

Game da halin da ake ciki, tawagar ta UNMISS ta ja hankalin daukacin bangarorin da wannan lamari ya shafa da su kai zuciya nesa, su kammala cikakkiyar yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya, duba da cewa, amfani da karfin tuwo ba zai warware sabanin da ke tsakanin sassan kasar ba. Hukumomin MDD dai na shan fama da kalubalolin da tashe-tashen hankula ke haifarwa a Sudan ta Kudu, lamarin da ya yi sanadiyyar raba kimanin fararen hula 650,000 da gidajen su, ba tare da samun wani tallafi ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China