Firaministan Sin Li Keqiang ya ce, ya kamata a dauki matakan samar da hanyoyin sadarwa na Internet masu saurin gaske, baya ga batun kirkiro da sabbin tunani game da raya harkokin sadarwa ta Internet, da kuma bunkasa sayayya ta Internet, da hada harkokin sadarwa da sauran sana'o'i bai daya, da kuma kirkiro da sabbin abubuwa.
A jiya Laraba ne dai, majalisar gudanarwar Sin ta ci gaba da fidda matakan da za a dauka, wajen kara saurin sadarwa ta Internet, matakin da ake fatan zai kara kawo jarin da yawansa ya kai kudin Sin RMB sama da biliyan dubu, wanda hakan zai sanya kasar ta Sin shiga wani sabon lokaci na raya tattalin arziki dangane da Internet. A yayin zaman taron majalisar gudanarwa da aka yi a jiyan, an bayyana cewa ya kamata inganta saurin Internet, da rage kudin da ake biya wajen duba shafin Internet. Hakan a cewarsa, baya ga kyautata zaman rayuwar al'umma, zai kuma rage kudin da ake bukata wajen raya sana'o'i ta Internet, kana zai yi amfani wajen raya manufar hada Internet da sauran sana'o'i bai daya, kuma zai inganta zuba jari, da sayayya, da ma sanya sabon kuzari a fannin raya kasa. (Bako)