in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Messi da Serena Williams sun tallafawa kokarin ilmantar da yara
2015-01-15 14:48:42 cri
Lionel Messi da shahararriyar 'yar wasan kwallon tennis Serena Williams, suna kokarin tallafawa wani shiri na sanya wasu daga cikin yara miliyan 58 dake sassan duniya daban daban samun damar karatu, ko komawa makarantu.

Wannan aiki mai taken '1 cikin 11', ya fara gudana karkashin kulawar Asusun yara ta MDD wato UNICEF, da hadin gwiwar asusun FC Barcelona, gami da kungiyar ROTA, a karkashin inuwar asusun kasar Qatar.

An ce makasudin wannan shiri shi ne taimakawa kashi 1 daga cikin 11 na yaran da shekarunsu suka dace da na lokacin karatu a firamare, wadanda suka kasa samun wannan dama sakamakon talauci su koma makaranta.

Kaza lika shirin zai taimakawa yara fiye da dubu 500 a Bangladesh, da Indonesia, da Nepal a matakin farko, daga bisani za a yada tsarin don taimakawa yaran karin wasu kasashe.

A matsayin wani bangare na shirin, an nuna wani fim na musamman na Messi da Williams, a yayin wasan da ya gudana tsakanin Barca da Atletico Madrid a ranar Lahadi.

A cewar masu kula da shirin, ana sa ran tara kudin tallafi da yawansa zai kai tsakanin dala miliyan 12, zuwa miliyan 15, a wani gwanjon kayayyakin al'adu da za a gudanar a birnin London cikin wata mai zuwa, wanda zai kasance aikin tara kudi na farko a karkashin shirin.

A cikin wani jawabin da ya gabatar, Messi ya bayyana cewa yana goyon bayan wannan shiri ne, domin ya yi imani cewar ko wane yaro na da hakki na samun damar cika burinsa.

A nata bangare Williams ta ce fatan ta shi ne, yawan yaran da ke rasa damar shiga makarantu zai ragu matuka da gaske.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China