Wannan sakamako dai ya daga matsayin Atletico zuwa ta 3 a teburin gasar da maki 50. Real Madrid ta ci gaba da rike matsayi na daya da maki 54, ya yin da Barca ke biye da ita da maki 53. Duba da 'yar tazarar da ke tsakanin wadannan kulaflika uku, akwai alamu dake nuna rashin tabbas ga kungiyar da za ta lashe gasar wannan kaka ta bana.
Ya yin wasan ranar Lahadi Leo Messi, da Luis Suarez, da Oscar de Marcos, da Neymar da Pedro Rodriquez ne suka ciwa Barca kwallaye dai dai, ya yin da Mikel Rico, da Aritz Aduriz suka ciwa Athletic Bilbao na ta kwallaye 2.
Kafin wannan wasa kuwa, Atletico Madrid ta baiwa kowa mamaki a wasan da ta buga da makwafciyar ta Real Madrid a ranar Asabar, wasan da ta lallasa Real Madrid din da ci 4 ba ko-daya. Wannan ne dai karon farko da Real Madrid ta sha kashi da irin wannan tazara mai yawa, tun cikin shekarar 1987.
Manazarta kwallon kafa sun nuna cewa, Atletico ta gwada kwarewar ta a dukkanin fannoni ya yin wasan na ranar Asabar. Kuma tun kan a tafi hutun rabin lokaci 'yan wasan ta Tiago Cardoso da Saul suka jefa kwallaye 2 a zaren Real, kana bayan dawowa hutun rabin likaci Atletico ta ci gaba da rike wasan, inda ta kara kwallaye 2 ta hannun 'yan wasan ta Antoine Griezmann da Mario Mandzukic.
A sauran wasannin da aka buga a makon jiyan kulaf din Getafe ya tashi 2 da 1 da Sevilla, matakin da ya baiwa Valencia damar kasancewa a matsayi na 4 a teburin gasar ta La Liga da maki 44. Ya yin da kuma Villarreal ke biya a matsayi na 5.
Koke ya ji rauni a wasan Atletico Madrid da Real Madrid
Daya daga muhimman 'yan wasan tsakiya na Atletico Madrid Jorge Merodio wanda aka fi sani da Koke, zai shafe wata guda naya jiyyar raunin da ya samu a cinya, ya yin wasan ranar Asabar wanda kungiyar sa ta lallasa Real Madrid da ci 4 da nema.
Mahukuntan Atletico sun ce Koke ba zai buga wasan zagaye na biyu na kulaflika 16 ba, wasannin da suka hada da wanda kulaf din zai buga da Bayer Leverkusen nan gaba cikin wannan wata, da ma watakila wasan su da Sevilla da kuma na Valencia.