in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Real Madrid na ci gaba da rikewa Barcelona wuta a gasar La liga
2015-05-05 11:12:19 cri
A yayin da gasar La liga ta kasar Sifaniya ke ci gaba da zafafa, yanzu haka Real Madrid na ci gaba da rike wuta, inda take biye daf da Barcelona, a kokarin ta na samun nasarar daukar kofin gasar na bana.

Yayin wasan Real Madrid na ranar Lahadin da ta gabata, kulaf din ya doke Celta Vigo da ci 4 da 2.

Tun da farko dai dan wadan Celta Nolito ne ya fara jefa kwallo a ragar Real, kafin kuma Tony Krooz ya farke kwallon. Sai kuma kwallon Hernedez wadda ta sanya real Madrid shigewa gaba. Sai dai kafin a kai ga hutun rabin lokaci, dan wasan Celta Santi Mina ya samu nasarar farke wannan kwallo, aka kuma tafi hutun rabin lokaci 2 da 2.

Bayan an dawo ne kuma James Rodriguez, da Hernandez suka kara kwallaye daidaya, aka kuma tashi wasan Real Madrid na da kwallo 4 Celta Vigo na da 2.

Javier Hernandez dai ya taka rawar gani a wannan wasa, kuma a baya ma shi ne ya ciwa Madrid din kwallaye 2, a wasan da ya baiwa kulaf din damar zuwa wasan kusa da na karshe, a gasar zakarun turai dake daf da kammala.

A ragowar wasannin da aka buga kuwa, Sevilla ta samu nasara kan Rayo Vallecano da ci 2 da nema. Sai kuma Malaga da Deportivo la Coruna da suka tashi wasa kunnen doki 1 da 1.

A daya bangaren kuma Almeria ta samu nasara Eibar da ci 2 da nema, a wasan da ya zamo na biyu ta na doke abokan karawar ta a gida, tun bayan da sabon kocin ta Sergi Barjuan ya kama aiki, inda kuma kulaf din ke kokarin tsallake siradin relegation. Shi kuwa kulaf din Eibar wasa daya ya samu nasarar lashewa, tun fara buga zagaye na 2 na kakar wasannin ta bana, wanda hakan ke barazana ga ci gaba da kasancewar kulaf din cikin gasar ta La liga a kaka mai zuwa.

A wasannin ranar Asabar 25 ga wata kuwa, Barcelona ta samu nasara kan Espanyol da ci 2 da nema. Ta hannun 'yan wasan ta Neymar da Leonel Messi. Shi ma kulaf din Atletico Madrid ya karfafa matsayin sa na kasancewa a mataki na 3 a teburin gasar, bayan da ya doke Elche da ci 3 da nema. Kaza lika Levante ta samu maki 3, bayan da ta doke Getafe da ci 1 mai ba haushi. Yayin da kuma Real Sociedad ta tashi kunnen doki maras ci ita da Villarreal.

A ranar Juma'a 24 ga wata kuwa, Athletic Bilbao ya samu nasara kan Cordoba da ci 1 da nema.

Yanzu haka dai Barcelona ce ta daya a teburin Laliga da maki 81, sai Real Madrid ta biyu da ma ki 79. Atletico Madrid ce ta 3 da maki 72, yayin da Valencia ke matsayi na 4 da maki 68. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China