in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Eden Hazard ne zakaran gasar kwararru ta Premier ta Bana
2015-05-05 11:11:33 cri
An bayyana sunan dan wasan Chelsea Eden Hazard, a matsayin zakaran 'yan kwallon gasar Premier na bana, wadda hukumar PFA ke zaba. Hazard, dan shekaru 24 da haihuwa, ya ci kwallaye 13, ya kuma taimaka wajen cin wasu kwallayen 8, a wasanni 33 da Chelsea ta buga a gasar Premier ta wannan lokaci. Sauran 'yan wasan da suka samu lambobin yawo daga hukumar ta PFA, sun hada da dan wasan Tottenham Harry Kane mai shekaru 21 da haifuwa, wanda aka baiwa lambar yawo ta dan wasa mafi kankantar shekaru, sai kuma 'yar wasan kulaf din mata ta Chelsea Ji So-Yun, wadda aka baiwa lambar karramawa ta 'yar wasa mafi hazaka a ajin mata.

Baya ga wadannan, akwai kuma 'yan wasan kulaf din na Chelsea 6 da suma suka samu yabo, ciki hadda mai tsaron baya Branislav Ivanovic, da John Terry, da Gary Cahill, da Nemanja Matic, da Eden Hazard da kuma Diego Costa.

Mai tsaron gidan Manchester United David De Gea, da kuma Philippe Coutinho na Liverpool, da Alexis Sanchez na Arsenal suma na cikin wadanda aka karrama. Kaza lika tsohon dan wasan tsakiya na kulaf din kasar Engila Steven Gerrard, da Frank Lampard, suma sun shiga wannan jadawali.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China