Cikin kudurin da aka gabatar yayin taron da ya kammala ran 19 ga wata, an ce, a halin yanzu, akwai manyan ayyuka da dama dake gaban mahukuntan Afirka ta Tsakiya, da suka hada da tabbatar da tsaron kasa, da farfado da tsarin zamantakewar al'umma, da komawar dalibai makaranta, da kuma samar da matsugunai ga 'yan gudun hijira.
Don gane da hakan ne ya kamata gamayyar kasa da kasa su nuna goyon baya, tare da samar da taimakon jin kai ga 'yan kasar yadda ya kamata, don ciyar da harkokin siyasa, da tattalin arziki, da zaman takewar al'umma gaba.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, babban taron kungiyar ta EU da ACP karo na 27 da ya gudana a birnin Strasbourg dake kasar Faransa tun ranar 17 zuwa ta 19 ga wata, ya samu halartar wakilai daga majalisun dokokin kasashen Turai, da na majalisun dokokin kasashen kungiyar ACP. An kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi Afirka ta Tsakiya, da hakar ma'adinan dake karkashin teku, da yaki da ta'addanci, da tsaron intanet, da kyautata ayyukan hukumomin kwastan, da kuma kawar da cutar kanjamau da dai sauransu. Har wa yau an zartas da kudurori da dama dangane da wadannan batutuwa. (Maryam)