in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi maraba da kudurin da kwamitin sulhu ya zartas game da jibge sojojin kiyaye zaman lafiya a Afirka ta Tsakiya
2014-04-11 20:58:15 cri
Kasar Sin ta yi maraba da kudurin da kwamitin sulhu ya zartas da shi dangane da jibge sojojin MDD na kiyaye zaman lafiya a kasar Afirka ta Tsakiya, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei a ranar 11 ga wata.

An labarta cewa, a ranar 10 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin jibge sojojin majalisar a Afirka ta Tsakiya domin kiyaye zaman lafiya.

Dangane da lamarin, Hong Lei ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, kasar Sin na fatan aikin kiyaye zaman lafiya da za a gudanar a Afirka ta Tsakiya zai taimaka wajen kwantar da kura a kasar. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China