in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An murkushe juyin mulki a kasar Burundi
2015-05-15 10:06:39 cri
Gidan rediyon kasar Faransa na RFI ya ce mataimakin jagoran yunkurin juyin mulkin da ya wakana a kasar Burundi Cyrille Ndayirukiye, ya tabbatar da dimbin hasarar da juyin mulkin kasar ya haifar.
Ndayirukiye ya bayyana hakan ne a daren jiya Alhamis, a daidai gabar da shugaban kasar ta Burundi Pierre Nkurunziza ke bayyana cewa ya riga ya koma gida.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter, Mr. Nkurunziza ya ce "ina cikin kasar Burundi, kuma na girmama kaunar da sojoji da 'yan sanda suka nuna wa kasar mu, kana na jinjinawa hakurin da jama'ar kasar ke nunawa."
A ranar 18 ga watan Maris na wannan shekara ne aka salami Godefroid Niyombare, daga mukamin shugaban hukumar leken asirin kasar Burundi, bayan nuna adawar da ya yi ga batun takarar shugaba Nkurunziza a karo na uku.
A kuma ranar 13 ga watan nan ne shugaba Nkurunziza ya tashi zuwa birnin Dar Es Salaam, fadar mulkin kasar Tanzaniya domin halartar taron koli na musamman, wanda kungiyar kasashen gabashin Afrika ta kira game da yanayin siyasa da kasar Burundi ke ciki. Da kuma yammacin wannan rana ne Godefroid Niyombare ya sanar da kifar da gwamnatin kasar mai ci, ta kafar wani gidan radiyo mai zaman kansa.
Sai dai jim kadan da aukuwar hakan, fadar shugaban kasar Burundi ta sanar da cewa an murkushe juyin mulkin da wasu suka yi yunkurin aiwatarwa.(Lami)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China