Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bukaci daukacin masu fada a ji a kasar Burundi, da su kai zuciya nesa bayan wani yunkuri na juyin mulkin soji, wanda a cewar fadar shugaban kasar bai yi nasara ba.
Da yake bayyana hakan, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce, Ban Ki-moon na fatan daukacin sassan da wannan batu ya shafa za su dauki matakan samar da daidaito, da wanzar da zaman lafiya, duba da hali na rashin tabbas da kasar ta Burundi ke ciki a yanzu haka.
A ranar Laraba ne dai tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Burundi Manjo Janar Godefroid Niyombare, ya tabbatar da aukuwar wannan juyin mulki, wanda a cewarsa ya kawo karshen mulkin gwamnatin kasar mai ci, kuma tuni aka fara shirin kafa gwamnatin rikon kwarya. (Saminu)