Magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Alhamis din nan ya bayyana matukar damuwar shi game da yanayin da ake ciki a kasar Burundi, tare da yin suka da kakkausar murya ga yunkurin juyin mulkin zababben gwamnati da karfin soja.
Tashin hankali dai ya yi ta cigaba bayan da jam'iyya mai mulkin kasar ta sake mai da shugaba mai ci yanzu Pierre Nkurunziza a matsayin 'dan takararta domin ya sake zarcewa a karo na uku lokacin babban zaben dake tafe a ranar 26 ga watan Yuni.
Shugaba Nkurunziza yanzu yana shirin kammala wa'adinsa na 2, abin da 'yan hamayya suka nace da cewa, takarar shi a karo na 3 ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar na shekara ta 2005.
Burundi dai ta fada cikin rudani tun daga ranar Laraba lokacin tsohon shugaban hukumar liken asiri na kasar Manjo Janar Godegroid Niyombare ya sanar ta kafar radiyo cewar, sojoji sun kifar da gwamnatin Nkurunziza, kuma masu ruwa da tsaki suna tattauna yiwuwar kafa gwamnatin rikon kwarya.
A game da hakan ne babban magatakardar MDD ya nuna damuwarsa matuka a kan abubuwan dake wakana a Burundin tun bayan wannan sanarwa ta tsai da Nkurunziza a karo na uku, musamman kuma sanarwar juyin mulki ta ranar Laraba, kamar yadda kakakinsa ya bayyana a cikin sanarwar da aka fitar.
Mr Ban yanzu ya bukaci al'ummar kasar da su kwantar da hankalinsu, tare da kaucewa duk wani abin da ka zama karya doka, haka kuma ya bukaci jam'iyyun siyasa da jami'an tsaro da su fito karara su nuna kin amincewarsu da duk wani aikin tashin hankali da guje wa wani shiri na daukan fansa, su kuma ja wa mabiyansu kunne.
Ya kuma ce, yana da cikakken imani cewa, kwamitin tsaron MDD zai yi nazarin duk wassu abubuwan da suka kamata dangane da Burundi domin samun mafita, in ji sanarwar. (Fatimah)